Mafi yawancin mutane, musamman masu amfani da wayar android, za ka same su suna amfani da wata software da ake kira da Launcher.Ita Wannan software ko kuma application ana amfani ne da shi domin kayata waya da kuma canza mata wasu daga cikin siffofin da take fitowa da su (misali yanayin yadda foton saman screen din wayar yake).
Duk da cewa wadannan applications suna da amfani wajen kayata waya, akwai wasu illoli sa sukan yi ma waya, wanda kuma ba kowa ne yasan sa wadannan illolin ba. A cikin wannan kasida zamu yi bayani daya bayan daya akan illolin da Launcher kan haddasa ma wayarka.

1. Hooking

A lokacin da ka dora Launcher sama da daya cikin wayarka to zaka ga cewa a duk lokacin sa ka danna malatsin home (na tsakiyar wayarka wanda ake minimizing da shi) za ka ga ta nuno maka duk wasu launchers din da ke cikin wayar sun fito domin ka zabi wacce kake bukata. A nan abin da ke faruwa shine, wayarka zata rasa wane salo zata yi amfani, domin ko wace launcher akwai yanayin yadda aka tsara ta. Wannan kan iya jaza wayar ta rikice, sanadiyyar hakan sai ka ga waya tayi hooking, ma’ana tayi tsaye cak, ta ki gaba ta ki baya har zuwa wani lokaci.Wani lokacin ma wayar ta kan dauke ne baki daya. Wannan kan iya sanya wane sashe na wayar ya Sami matsala

2. VIRUS

Sanin kowa ne akwai hackers wadanda kullum niyyarsu shine su yada virus wacce zata ita haddasa wata matsala ga kwamfutoci ko kuma wayoyin mutane. Sukan tsaya su duba ne su ga wane abu ne mutane ke bukata kuma suka fi yin download dinsa, sai su dauki wannan abun su gurbata shi da virus ta yadda duk wanda yayi download din shi to wayarsa ko computer zata kamu da wannan virus din. Kuma kowa ya sani akwai illoli da dama da virus ke haddaswa kamar yadda muka bayyana a cikin wannan kasidar tamu.
Dukkan wadannan illoli guda biyu da muka dawo na Launcher ka iya jaza sai anyi ma wayarka flashing (shiga domin ganin yadda zaka yi flashing/Restore da kanka). Shawara anan itace, idan lallai kana bukatar yin amfani da Launcher, to ka tabbatar bata wuce daya ba a cikin wayarka, amma tara lauchers da dama zaya jawo maka matsala babba. Domin tabbarwa cewa Launcher dinka bata dauke da Virus, kayi download dinta da kanka daga Google Play Store.