Sau da
yawa za mu batar da abubuwan mu da muke amfani da su na yau da kullum
kamar su mukullai, waya, wallet da sauransu, ko kuma ma mu ajiye mu
manta inda muka ajiye, mu yi ta faman nema.
Ita wannan fasaha mai suna Trackr Bravo kacokat din ta an yi ta saboda magance wannan matsala.
An yi
fasahar ne a gida biyu. Akwai manhaja (App) na waya da kuma kanana
na’urori (wireless devices) da ake makalawa a kan abunda ka iya bata
kamar su wallet ko mukulli, kai har abun hawanka ma idan ka so.
Yadda ake
amfani da shi shine: idan abu ya bata, za ka bude manhajar ka ta wayar
android ko iPhone ka latsa gurin da aka tanada. Wayarka za ta nuna maka
inda abun yake, idan gurin da nisa, za ta yi amfani da ‘Google Maps’
wajen nuna maka hanyar zuwa wajen. Idan a kusa ne kuma za ka iya sanya
wayarka ta yi kira ga na’urar, ta yadda za ta yi kara kamar na kiran
waya.
Bugu da kari, idan ita wayar ce kanta ta bace, latsa na’urar kawai mutum zai yi sai ta fara kara.
A yanzu
dai wannan manhaja da nau’ra ana Sayar da su ne tsakanin dalar Amurka 30
da kuma 120, kwatankwacin adadin na’urorin da mutum yake bukata.
0 Comments