YADDA ZAKA KARE ACCOUNT DINKA NA
FACEBOOK DAGA MACUTAN
YANAR GIZO
Assalamu’alaikum
warahmatullahi wa barakatuhu
Mahimin abu wanda galibin
mutanen da keyin facebook
basu san da shiba shine yadda
zasu kare facebook dinsu daga
mutanen da suka kware wajan
kwatarwa mutane account a
facebook
Wasu kuma sun sani amma
saboda hatsarin hanyar yasa
sukayi watsi da ita.
Wasu kuma tuni suka dade da
bin wannan hanyar domin
ganin sun ba account dinsu
kariya.
HANYOYIN BADA KARIYA GA
FACEBOOK SUNKAI KAMAR KASHI
3.
1. Hanya mafi tsauri itace wacce
zakai amfani da wasu code
wadanda facebook zasu baka,
Matsalarta itace idan ka manta
wadannan code din to account
dinka ya tashi aiki, saboda aduk
lokacin da zakayi login sai sun
tambayeka wannan scurity code
din da suka baka.
2. Zaka zabi kalar browser da
kake aiki da ita kasa musu, sai
su baka wasu code wadanda
aduk lokacin da za’ai login din
account dinka da wata browser
nanma sai ansa wannan code
din sannan account din zai
bude.
3. Wannan itace hanya mafi
sauqi kuma mafi akasari
mutane yanzu ita suke bi domin
bada kariya a ccount dinsu na
facebook
dan haka nima yanzu akanta
zan maku bayani.
YADDA HANYAR TAKE KUWA
SHINE…
Idan kana amfani da ita to duk
lokacin da wani yake kokarin
hawa maka account batareda
umarninka ba to facebook
zasuyi gagawar sanar da kai ta
hanyar sakon text message
zuwa lambar wayarka
dan haka da zarar sun sanar da
kai to wani yana kokarin
hawama account saika maza ka
hau ka dauki matakin canja
password.
YADDA ZAKA CANJA PASSWORD
br /> Ka hau facebook dinka ka
tafi can kasa, ka shiga inda kaga
an rubuta setting & privacy
bayan yabude saika shiga
General, bayan ya bude saika
zabi password kashiga, idan
yabude zasu umarceka dakasa
password dinka a box din
farko, a box na biyu saikasa
sabon password din daka ke
son canjawa, a box na ukuma
kasa sabon, sannan kadanyi
kasa kadan zakaga change
saika shiga, to da zarar ka canja
kaga ka gama da wancen mai
kokarin hawama account.
YADDA ZA’A SAKA WANNAN
TSARIN br />
Idan ka hau facebook dinka
saika tafi zuwa can kasa ka
shiga inda kaga an rubuta
Settings &Privacy
idan ya bude saika zabi security
ka shiga, da ya bude saika zabi
‘Text Message Login
Notifications da E-mail
Login Notification.
zakaga daga gabansu kadan
akwai blue din rubutu ansa
‘Desable to saika hau kanshi
kayi ok! da yagama Loading
zakaga ya koma ‘Enable Amma a
Text Message Login
Notifications, saika sake
comfirm na password dinka
shikenan daga nan kaga ma
Kuma ko waye zaiyi login din
account dinka sai ansanar da
kai ta Lambar wayarka, koda
kuwa kaine kayi login din da
wata sabuwar browser
matukar layin da ka bude
facebook yana akan wayarka to
sai sun sanar da kai ko ta email