Daya daga cikin tambayoyin da jama’a suke yi a kowane lokaci shi ne ya mutum zai yi a lokacin da ya rasa kayan da ya ajiye a cikin memory SD Card na wayarsa, Camera a sanadiyar kankare memory (formatting) ko kuma an goge abin da ke ciki (deleting).
Amma kafin in fadi yadda ake yin wannan aiki ko kuma manhajoji (software) da ake bukata yana da kyau in sanar da jama’a yadda shi wannan memory yake da kuma yadda ake lura da shi.
Memory dai wani irin mazubi ne da aka yi shi domin ya ba mutum damar ya iya yin ajiyar kayan da aka yi su da wutar lantarki (electronic data) wanda ya hada da hotuna da rubutu da surkulle da duk wani abu da ake iya adana shi a cikin computer.
Wadannan memory yana da yanayi mabanbanta dangane da yadda ake yin sa da kuma tsarin yin sa, sai dai mafi shahara shine wanda ake yin amfani da shi a mafi yawan wayoyin tafi da gidanka na zamani.
A baya, mafi yawan kanfanonin da suke kirkirar wayoyi ko kamara kowa na yin irin nasa memory, dangane da girma ko fadi, wanda ya sanya akwai matsala sosai yadda memorin wani kamfani baya aiki a wata na’ura da ba tasa ba.
A baya wannan memory ya na da tsada matuka, ga shi kuma yana da wahalar samuwa a kasashen mu, ga shi kuma ba shi da girman wurin kwasan bayanai, amma Alhamudu Lillahi a yanzu wannan ta kau domin ana samu memory wanda a kalla yana iya daukar Gig dubu shi kadai.
Daga cikin abin da yake damun jama’a shi ne yawan lalacewarsa da kuma rashin sa’a wurin gogewar abin da ke ciki. Mutane da dama suna manta cewar Memory shima kayan kwamfuta ne, kuma yana iya lalacewa kowane lokaci, musamman idan aka yi rashin sa’a wanda yake rike da shi bai iya lura da shi.
Wani lokaci ba wai memorin ya lalace ba ne, a a an sami matsala ne da inda aka saka shi. Misali zai iya yuwuwa ka sami wayar da take daukar memory da yake da tsarin ajiyar bayanai na FAT (File Allocated Table) to idan ka saka shi a cikin wata wayar da baya daukar wannan tsarin sai ka ji ta fada maka cewar wannan memorin yayi dameji.
Ko kuma wani lokaci zaka ga duk abin da ke cikn memorin ya ki budewa ko kuma ya nuna alamar lalacewa wanda wannan shima ba yana nuna cewar memorin ya daina aiki ba ne ko kuma kayan cikinsa sun lalace. Shima wannan yana da danganta ne da irin File Sysmem din da aka ajiye kayan tun farko.
Wani lokaci kuma zaka ga ka dauko kaya daga cikin kwamfuta ko wata wayar amma da zarar ka tashi budewa sai ka ji ya na fada maka cewar Unsupported format wannan shima ba yana nufin cewar memorin ya lalace ba ne yana maganar cewar wayar bata da application din da zai bude.
To duk wadannan ba abin da za mu yi magana ba ne a kai. Muna son muyi magana ne ga mutum da cikin rashin sani ko ma ganganci ya goge abin da ke cikin memory na wayarsa kuma yana son ya sake dawo da wannan kaya.
A tsari irin na bature da kuma yadda yayi kayan ajiya na kwamfuta wato storage devices yana da kyau jama’a su sani cewar duk abin da ya taba shiga cikin memory na kwamfuta ko waya ko flash har abada yana nan, koda kuma an goge shi ko an yi formatin lallai yana nan, kuma za a iya dawo da shi. Sai dai inda gizo ke saka shi ne dame ya kamata in yi amfani wurin dawo da wadannan kayan?
Akwai hanyoyi mabanbanta da jama’a suke yin amfani da su wurin dawo da kayan da suke cikin memory, kadan daga ciki shine ta yin amfani da shafukan intanet domin samun biyan bukata. Sai dai a nawa shawarar ban cika son jama’a suna yin amfani da wasu shafukan intanet wurin irin wannan aiki ba, kasancewar mafi yawan irin wadannan shafuka na yan yaudara ne da zamba da kuma zubawa mutane miyagun virus cikin wayarka ko kuma kwamfutar ka. Amma akwai na kirki sai dai mafi yawansu sai ka biya kudi.
A wannan karatun zan nuna mana wadansu manhajojin kwamfuta na kyauta kuma garanti ga duk wanda yake son yayi amfani da su wurin dawo da kayan da suka bace a memorinsa. Idan memorin yana cikin waya ne ko kuma cikin kamara kuma idan ka hada shi da kwamfuta baya nuna memorin to yana da kyau ka ciro memorin daga cikin inda ya ke ka saka shi a cikin Card Reader domin fara yin wannan aiki.
Abin kiyayewa shi ne, tunda da kwamfuta zaka yi wannan gyara to ka sani mafi yawan kwamfutar da muke amfani da ita a wannan kasa ta mu kashi 60 suna dauke da virus mai cinye kayan kwamfita ma mayar da su shortcut, to, amfani da irin wannan kwamfutar akwai hatsari, saboda haka ka sami kwamfutar da ka san tana da anti-virus mai kyau, kuma ana updating dinsa kafin ka zura shi.
Wani hanzari ba gudu ba, idan kasan akwai wadansu kaya a cikin memori din to yana da kyau ka kwashe su ka zuba su a cikin wani folder domin kada garin so ka dawo da baya ya zama suna da suna iri daya da wannan sai ya daura a kansa.
Wadannan dai sune kadan daga cikin abin da zan iya jan hankali a kai kafin in nuna mana software din da zan yi magana a kai. Amfani da wadannan application ba wani wahala ya ke da su ba, da farko dai dukkansu kyauta ne kuma suna yin aiki sai kamar yadda ya kamata duk da de ba wai zan fadi mataki bayan mataki bin kowane daya daga cikin su ba ne, sai dai zan fadi shi application din da kuma amfanin sa.
1 Recuva (Na aiki a Windows ne kawai)
Wannan application na Recuva(version 1.5) nauyin sa 4.02MB ne kuma kyauta ne, yana aiki a kwamfutar da take da operating system na Windows ana kuma iya saka shi a Windows 2000 zuwa sama. Idan kana son ka dawo da files din ka dake cikin memory din ka.Zaka saka memorin a cikin Card Reader sannan ka zura shi a cikin kwamfutar da ka yi installing wannan application na Recuva, sai ka tashe shi (recuva) sai ka zabi shi memori din a cikin jerin manyan kwakwalen da suke jikin kwamfutar. Sannan sai ka taba maballin Scan.
Zaka bashi lokaci don zai dawo da kayan da aka goge a cikin sannan zai baka maballin da aka rubuta Recover sai ka taba shi domin ya dawo maka da wanda kake so.
2 Pandora Recovery (Na aiki a Windows ne kawai)
Pandora Recovery shi ma kyauta ne yana da girman 3.12MB, yana aiki a kwamfutar da aka sa mata Windows kuma wacce Operating System dinta ya fara da Windows XP zuwa sama. Shima yana aiki ne kamar yadda recuva, wato za a ciro memorin a saka a cikin Card Reader sai a saka a cikin kwamfutar da aka yi Installing Pandora Recovery. Sannan zai zabi kodai yayi Quick Scan ko Deep Scan. Shi na Quick Scan ga wanda ya ke son ya dawo da abubuwan yayi deleting ne amma wanda yake son ya dawo da wadanda aka yi formatting shi zai amfani da Deep Scan.Bayan ya gama scanning za ka iya zaba tsakanin kodai ka yi amfani da Pandora Recovery Wizard sai ka yi amfani da sharudda da zai rika fitowa kana zaba har ka gama, ko kuma ka yi right click ka zabi abin da kake son ka dawo da su.
3 Stellar Phoenix Mac Photo Recovery (Na aiki OS X ne kawai)
Shi Stellar Phoenix Mac Photo Recovery (version 6.0) girman shi 13MB ne, kuma yana aiki ne a kwamfutar da take da Operating System na OS X 10.5 ko sama da haka. Ana bukatar wanda zai yi amfani da wannan manhajar da ya yi amfani da Card Reader shi ma, sannan ya kunna wannan application.Za ka iya yin amfani da wannan manhajar domin dawo da hotuna ko bidiyo ko sauti ta hanyar zabar me kake ya dawo maka. Idan ka zaba sai cewa manhajar ta yi bincike wato sanning ta hanyar taba Scan Now ko kuma taba Advanced Scan domin yin bincike mai zurfi.
Mutum zai iya zabar kayan da ya ke son ya dawo masa da su musamman wadanda deleting dinsu aka yi deleting dinsu, amma ga wanda yake son ya dawo da kayan da formating dinsu aka yi sai idan ya biya su kudi.
Wannan manhajar yanzu akwai irinta ga wanda ya ke da kwamfutar da take da manhajar Windows.
4 PhotoRec (Na aiki da DOS, Windows 9x zuwa Sama, Linux da OS X)
Shi wannan manhajar ta PhotRec na kyata ne kuma hadin gwaiwar masana ne suka kirkire shi, shi yasa yake aiki a cikin kowace kwamfuta. Yana da girman 9.4MB. Yana zuwa tare da shi wannan PhotoRec wani application a cikinsa mai suna TestDisk wanda shi wannna TestDisk yana dawo da partition din da aka yi deleting.Shi yana bukatar kafin ka fara amfani da shi ka zabi wani tarin file ne memorin ya ke da shi misali ko FAT ko NTFS, sannan ka zabi shi memory din sannan ka ce yayi binciken wato Scan. Bayan ya gama recovery din sai ka zabi wurin da kake son a jiye kayan da ya dawo maka.
Wannan sune kadan daga cikin application da zan kawo muku wanda zasu taimaka maku wurin dawo da kayan da kuka goge ko kuma kuka rasa sakamakon an yi formating Memory.
Mu hadu a wani darasin na gaba.
TURA WANNAN LABARI A WHATSAPP
0 Comments