Mene dalilan da suke sa wayata ke yawan makalewa? Wannan ita ce tambayar da miliyoyin jama’a masu amfani da wayoyin wannan zamani suke yawan yi. Mu sani lokacin mai tsawo ya riga ya shude na amfani  da waya wacce bata makalewa kamar lokacin da aka yi wayoyi kirar Nokia 3310 ko Nokia 1100. Yanzu muna amfani da wayoyin komai da ruwan ki ne (smartphones), waya wacce take dauke da manyan manhajoji wadanda suke aiki tamkar babbar kwamfuta. Irin wadannan manhajoji suna bukatar sarari da kuma yalwa wurin tafiyar da al’amarinsu. A yanzu wayoyin smartphone suna dauke da babbar manhaja (Operating System) irin su Android da iOS da kuma Windows duk da cewar akwai wadansu manyan manhajojin da ake kirkirar waya da su amma dai wadannan guda ukun su suka fi shahara a wurin mutane.
Saboda haka amfani  da irin wadannan wayoyi suna bukatar kayan aiki (HARDWARE) masu inganci. Baya ga shi kanshi OS din ana kuma samun kananan manhajoji wadanda su kansu suna bukatar sarari na musamman domin yin aiki. To, makalewar waya yana faruwa ne a lokacin da wata manhaja (app) ta yi kokarin ta tashi tayi aiki, sai ya kasance irin Hardware da take bukata tayi amfani ko dai bai ishe ta ba, ko kuma sararin da take bukata tayi amfani da shi ya cika. To duk lokacin da makalewar ta faru zaka samu ita wayar bata iya baka dama ka yi wani abu da ita sai idan ta dawo hayyacinta.
Wani lokaci dan makalewar da waya take yi bai kamata mutum ya damu kansa ba, domin wadansu manhajojin sai sun daidaita sosai kafin su fara aiki. Amma idan ya kasance kowane lokaci wayar hakan take yi to lallai akwai katuwar matsala kuma yana da kyau mutum ya bi abubuwan da zamu ambata a cikin wannan mukalar.

1.    Sayi waya mai babban RAM

Daga cikin abin da yake yawan sa smartphone take makalewa shine rashin isasshen RAM (Random Access Memory) a jikin wayar. Kodayake mafi yawan jama’a da suke amfani da waya ba su san da wani abu wai RAM ba, wadanda kuma suka sani suna dauka cewar matsayinshi daya da memory na ajiyar hoto ko sauti.
Aikin da RAM ya ke yi a jikin kowace na’ura shine ya ba ma application sarari da zai hau yayi aiki. Shi yasa RAM ke taka muhimmiyar rawa wurin hanawa ko sanya waya ta rika makalewa. Duk lokacin da mutum ya kunna waya to OS din wayar zai hau kan RAM din ne ya zauna. Haka idan ka tashi wani app shima yana bukatar ya sami wani bangare a jikin RAM din ya zauna, saboda haka idan ka tashi manhajoji da yawa sai ya kasance wayar ta rasa wurin da zata ajiye manhaja sai ta fara makalewa.
Mataki – A yanzu haka akwai wayoyi da ake yin su da manyan RAM, kuma suna da arha sosai, idan mutum mabukacin yin amfani da application masu karfi kamar su game da makamantansu, sai mutum ya sani waya mai girman RAM ya kara da ita.

2.    Rage manhajoji masu aiki a-kai-a-kai

Kamar yadda muka ambata cewar RAM shike taka muhimmiyar rawa wurin sa waya ta rika makalewa, wannan yake nuna mana cewa duk lokacin da waya ta makale zai yiwu manhajojin da suke aiki a-kai-a-kai suna da yawa.
Saboda haka yake da kyau mu rage irin wadannan manhajoji musamman irin wadanda suke yin aiki ta karkashin kasa (background) domin akwai manhajoji da dama da suke yin irin wannan aikin kuma bamu sani ba, saboda haka zaka iya goge irin wadannan manhajoji ta buda su da kuma tsayar da wadanda suka cancanci a tsayar.
Mataki – ka shiga settings > Apps > Running App. Sai ka duba wanda ya fi cinye RAM ka tsayar da shi, amma kada ka tsayar da Android System ko Google Play Services

3.    Yin updating App kodawane lokaci

Mutum ya rika ziyartar shafukan da suke da alhakin lura da manhaja domin ganin ko an fitar da sabuwar manhajar da yake amfani da ita. Misali wadanda suke amfani da wayoyi kirar Android zasu shiga Google Play, wadanda suke amfani da wayoyin iPhone su kuma su shiga iTune App Store domin ganin ko wadanda suka yi manhajojin da suke amfani da wayoyinsu sun sabunta su. To idan sun sabunta su sai ka sake saukarwa, domin yin haka zai kara taimakawa wayar wurin ganin ta yi aiki kamar yadda ya kamata.
Mataki – Duk lokacin da aka sabunta sabon manhaja (App) masu yi suna yin la’akari da wayoyin da aka fi amfani da su, da kuma suna lura da yanayin RAM da app din nasu yake bukata.

4.    Goge abubuwan da manhaja ta tara (clear cache)

Duk lokacin da mutum ya bude manhaja domin yayi amfani da ita, musamman irin wadanda suke bukatar internet domin samo bayanai ko labarai, suna tara wadannan bayanai a wani wuri na musamman, irin wadannan kaya da take tarawa a na kiransu da caches. Misali lokacin da mutum ya saukar da manhajar WhatsApp to idan ta fara aiki duk abin da ya sauko cikin wayar na rubutu to yana taruwa ne, sai idan ya taro sai application din ya rika makalewa. To, goge caches baya goge app din a cikin waya, sai dai yana mayar da application ya koma tamkar sabon sakawa ne a cikin waya.
Mataki – Settings > App sai mutum ya taba application din zaiga clear cache. Amma kamar na Android clear data zai fi taimakawa, dai yana da kyau kayi backup na kayan cikinsa kayin ka goge.

5.    Kashe waya

Kashe waya a kalla sau daya duk wani tsawon lokaci a sake kunnata, misali mutum ya ruka kashe waya duk safiya ko duk dare yin hakan zai rika wartsakar da wayar daga wadansu manhajoji da suke yin aiki amma mutum ya manta bai kashe su ba.

6.    Cire SIM da batirin waya

Yana da kyau a kalla a wata mutum ya sani wata rana da zai kashe wayarsa kuma ya cire batiri tare da SIM domin yin hakan yana taimakawa wurin cire kurar da wutan lantarki take tarawa, yin hakan na da matukar amfani, kuma yana rage makalewar waya.

7.    Girke (Install) App a ma’ajiya na waje (External Memory)

Mutane da dama basa su cika kiyaye a wane wurin app din da suke saukarwa yake girka kansa ba bayan sun saukar da shi. Kuma mutane da yawa basa yin la’akari da cewa duk inda manhaja ta samu wuri ta zauna to tana kara taimakawa wurin tafiyarta da sauri ko kuma makalewa.
Sau tari ga al’ada na su wayoyi suna girke manhajoji a cikin ma’ajiyar waya da ta zo da shi wanda ake kira da Internal memory. A wani lokaci barin wadannan manhajoji a cikin Internal Memory yana kara taimakawa wurin waya ta rika makalewa. Shi yasa yake da kyau mutum ya samu ma’ajiya ta waje (External Memory) ya sakawa ita wayar sannan ya kwashe manhajojin da suke cikin wayar ya mayar da su kan SD Card din sa.
Mataki – idan kana son ka canza inda wayarka ke girke manhajoji zake shiga Settings > Storage > Default write disk > Select SD Card. Abin kiyayewa a nan wadansu wayoyin na su ya sha banban da wanda muka nuna saboda haka sai mutum yayi dan bincike kadan idan nashi ba haka yake ba.

8.    Canza mazaunin girkakkun manhajoji daga Internal memory zuwa SD Card

Akwai damar da mutum yake da ita na canzawa girkakkun manhajoji da aka riga aka ajiye su a cikin wayar zuwa cikin ma’ajiya ta waje. Kamar yadda bayani ya gabata kana bukatar canza musu wuri domin ba wayar damar ta rika yin aiki ba tare da samun wata matsala ba. Canza musu wuri daga Internal Memory zuwa External Memory zai hana wayar makalewa.
Mataki – mafi yawan manhajojin da ake iya canza wurin da aka girke su ana samunsa ne a Settings > App

9.    Daura manhajoji daga asalin tushen su

Mu a kasashen mu na Afirka nan ne zaka samu mutum na amfani da waya amma kuma bai san cewar kowace waya tana da asalin inda ake samun manhajojinta ba. Misali zaka samu mutum akwai manhajoji masu yawa a wayarsa amma kuma duk daga wata waya aka turo masa.  Saka manhajoji ta hanyar turawa na taimakawa wayar ta rika aikata wani aiki wanda ba a sata ba, ko kuma ta rika makalewa a kowane lokaci.
Dukkan wayoyin android ana samun manhajojinsu a Google Play, su kuma masu iPhone suna amfani da iTune App Store saboda haka baka bukatar komai illa imel tare da su domin saukar da manhajojinsu. Duk mutumin da yake amfani da application na turawa baka raba wayarsa da virus.

10.                Saka Manhajar kariya da  Virus (Antivirs Software)

Virus suna taka muhimmiyar rawa wurin sa waya ta rika makalewa kowane lokaci. Su kuwa virus din nan ba kamar hoto ba ne ko bidiyo da mutum zai iya ganinsu a cikin wayarsa ya gane kuma ya fitar da su. Virus wadansu boyayyun manhajoji (application) ne da suke shiga cikin kwamfutar mutum ko wayarsa ta hanyar amfani da kwamfuta ko wayar da ke da virus din ko kuma shiga gurbatattun shafuka a internet, ba tare da shi mai wayar ko kwamfutar ya sani ba.
Akwai antivirus na kudi da na kyauta a cikin wadancan dakuna da ake samun manhajoji a ciki, wanda mutum zai iya saukarwa domin kariya daga virus din.

11.                Goge manhajojin da ba a aiki da su

Za a iya samun wani lokaci mutum ya saukar da manhaja a cikin wayarsa amma kuma bai taba amfani da ita ba. To irin wannan yana da kyau mutum ya duba duk wata manhaja da ya san cewar ba ya amfani da ita ya fitar da ita da ga wayar sa. Hakan zai taimaka wurin kara samun sarari a cikin wayar ko ya karawa wayar kuzari.

12.                Goge abubuwan da ba a bukatarsu

Ajiyar hotuna da sauti da bidiyo a akan waya bukata ce ke kawo su, amma kuma suma za su iya taimakawa matuka wurin sanya wayar ta rika makalewa. Shi yasa yake da kyau idan mutum yana da hotuna da sauti ko bidiyo da yasan ya gama amfani da su to ya cire su daga wayar domin karawa wayar sararin da zata bukaci tayi aiki cikin sauri.

13.                Fahimtar manhajoji masu iya rike waya

Akwai manhajoji da dama wadanda a ka’idarsu sun fi sauran manhajoji amfani da sarari na waya. Kama daga sararin da ita wayar take bukata wurin ajiyar manhajoji a RAM ko kuma sararin ajiyar ayyuka Memory. Mafi yawan manhajijin wasannin kwamfuta wato Games suna daga cikin irin wadannan manhajoji, kuma duk lokacin da mutum ya tashi irin wadannan manhajoji ya lura da kyau zai ji wayar tana yin zafi da kuma nauyi wurin gabatar da wadansu aikace-aikacen.
Domin sanin wane app ne yake cinye memory mutum zai shiga Settings > Apps (ko Memory) > Running Apps. A nan mutum zai ga wace manhaja ce ke cim memory kuma nawa ta diba kuma nawa ta rage.

14.                Barin wurin shakar iska ga ma’ajiyar waje

Kamar yadda muka ambata cewa dauko manhajoji daga Internal memory zuwa External memory yana taimakawa waya wurin yin sauri, wannan ba kuma shi ke nuna maka cewar ka cika SD Card din ka fal da kaya har a rasa wurin ajiya ba. A kalla ana son mu rika bawa SD card din mu sarari da zai rika shakar iska domin samun saukin daukowa da ajiye abu a cikinsa.

15.                Resetting na waya

Wannan shine mataki na karshe da mutum zai iya yi idan ya gwada dukkanin wadancan hanyoyi da muka ambata a baya. Yin factory reset shi ne ya goge dukkan wani app da aka sakawa wayar da kuma wadansu data da aka ajiye a cikin internal memory na wayar. Yin haka zai sanya wayar ta dawo kamar sabuwa, duk wasu matsaloli dasuke sa ta daina aiki ko rikewa zasu rabu da ita.
Wannan shine karshen bayanai da zamu yi game da dalilai da suke sa waya ta makale da kuma hanyoyin da ake bi domin ganin an magance. Shin wanne ne cikin wadannan hanyoyi ka taba gwadawa? Ku bamu labarin yadda wayoyinsu suke yi da kuma hanyoyin da kuke bi domin magancewa.