A wani rahoto da hukumar kula da harkoki SADARWA ta Nigeria wato NCC ta fita, ta bayyan cewa ‘yan Nigeria masu amfani da kafar SADARWA ta internet na kashe kudi da suka haura Naira Milyan dubu 194 (N194 bn) a ko wane wata wajen sayen data da suke amfani da ita wajen shiga internet. Wannan rahoto dai bai zo mana da mamaki ba duba da irin yawan ‘yan Nigeria da ke amfani da wannan kafa ta Internet wanda kuma ko a wace rana wannan yawan kara karuwa yake. Nigeria ita ce kasa ta 5 a duniya wajen yawan masu shiga kafar internet kamar yanda wani rahoto ya nunar a baya.
Kamar dai yanda rahoton NCC na baya bayan nan ya nuna, akwai sama da mutum milyan 149 da dubu 500 da ke amfani da wayoyin tafi da gidanka (wato mobile phones). Daga cikin wadannan mutane masu amfani da wayoyin kuma, mutum milyan 92 na amfani wayiyinsu domin shiga kafar SADARWA ta internet.
Kamfanonin sadarwa da suka fi samun kudi ta wannan hanya sun hada MTN, Glo, Airtel da kuma 9Mobile. A cikin wadannan kamfanoni, MTN na da mutane milyan 58, Glo na da mutune milyan 37, Airtel na da mutane milyan 34, 9Mobile kuma na da matane milyan 19 masu amfani da internet. Sauran kason masu amfani da internet din kuma suna amfani ne da sauran kananun kamfanonin da ke samar da internet connection.
Idan dai ba’a manta ba, wani rahoton bincike da aka fitar ya nuna cewa kamfonin layukan sadarwa a Nigeria na samu kudi da suka haura Naira biyan 2 da milya dubu 200 (N1.2 trillion) a duk shekara wajen samar da ayyuka ga abokan huldarsu. Wannan ne ya sanya gamayyar kungiyar kula da harkokin sadarwa ta duniya wato ITU ta bayyana a baya cewa, Nigeria ce kasar da kamfanonin  sadarwa suka fi nuna bukatar shiga domin da ta fi ko wace samun ci gaba a duniya.
To yanzu kai mai karatu nawa ka ke kashewa duk wata a kan data ta internet?