Da yawa daga cikin mutane, musamman ma masu amfani da wayoyi kirar android, sukan ji a ko da yaushe ana zance a kan Rooting, ko kuma idan sun bukaci yin wani abu da wayarsu sai ace sai an yi Rooting din wayar kana ta iya yin wannan abin. Akwai mutane da yawa masu son yi ma wayarsu rooting to amma saboda wani shakku da akan sanya musu cewa wani abu zaya iya faruwa ga wayoyinsu, sai ya zamto suna jin tsoron yin hakan. A cikin wannan kasidar, zamu yi sharhi akan wannan abu da ake kira da ROOTING, amfaninsa, akasin hakan, da kuma dalilan da zasu iya sanyawa ku yi Rooting din wayoyinku.
Minene Rooting?
Dangane da masu amfani da wayoyin android, Rooting dai wata hanya ce da ake bi domin debe duk wani shinge ko kuma iyaka da kamfanonin wayoyi sukan sanya ma wayoyin dangane da irin ayyuka ko kuma abubuwa da mutum zaya iya yi da wadannan wayoyin. Dalilin da ya sanya wadannan kamfanoni ke sanya irin wadannan shingaye akan yanda za’a iya amfani da wayoyinsu shine don su bambanta wayoyin da ko wanensu ke fitarwa, ta yanda zaka iya bambance abubuwa da zaka iya samu a cikin Gionee da kuma waya kirar Tecno. Wani dalilin kuma shine, kamar yanda wata kila kuka sani, manhajar da ke tafiyar da wayoyin android (Wato Operating System) da Google ke samarwa kyauta ne, wannan manhajar kuma tsarinta shine, tana baiwa mutum dama yayi duk wani abu da ya ga damar yi da wayarsa ko kuma computarsa. To su kuma kamfonin suna ganin cewa idan basu sanya wannan shingaye ba, to mutum zaya iya lalata wayarsa da kansa, ta hanyar shiga wani waje mai hatsari wanda kuma ba lallai bane ace ya san abin da yake nufi ba. Amma kuma wannan mataki nasu ya sanya mutane basa iya yin wasu muhimman abubuwa da wadannan wayoyin har sai sun debe wadannan shingayen (wato sai sun yi Rooting).
Hatsarin ya ma Android Rooting
A mafi yawancin lokuta, hatsarurrukan da ake ta cewa Rooting din wayar android na haddasawa dukkansu kawai ana ruruta su ne, domin sau da yawa wadannan abubuwa ana fadarsu ne kawai domin a tsoratar da masu bukatar yin wannan abu. Abu na biyu kuma shine matakin da kamfanonin da ke samar da wadannan wayoyi kirar android na cewa, duk wanda yayi Rooting din android dinsa, to ba zasu bashi garanti (guarantee) na wayar ba, kuma duk wata matsala da wayar ta samu to su babu ruwansu ba zasu yi masa wani taimako ba.
Amfanin yi ma waya Rooting
Tun da dai kuka ga a ko da yaushe yawan mutanen da ke yi ma wayoyinsu Rooting yana ta karuwa, tabbas kun san cewa akwai wasu kwararan dalilai da suka sanya mutane kan yi hakan. Wadannan dalilai basa rasa nasaba da irin Karin dama da mutane ke samu ta yin wasu abubuwan da wayoyinsu wanda asali ba zasu iya yi ba. Kadan daga cikin wannan abubuwa sun hada da:
  1. Bada cikakkiyar damar shiga ko ina a cikin wayar
  2. Baiwa mutum dama yayi duk wani abin da yake bukatar da wayarsa
  3. Baiwa mutum karfin ikon dama da zaya iya cire wasu applications wadanda ke zuwa tare da wayar
  4. Baiwa mutum karfin ikon da zai iya cire irin wadannan Virus din masu kama waya, wadanda ke sanya wasu hotuna a saman screen ta yanda mutum ba zai iya yin wani abu da wayar ba har sai ya zare batiri ya sake kunna wayar
  5. Baiwa mutum damar sanya wata manhajar (Operating Sytem) daban da wanda kamfanin wayar suka sanya ma wayar
  6. Ga wayoyin da basu iya daukar screenshot (hoton screen), Rooting zaya ba su damar mutum yayi hakan
  7. Yi ma waya Rooting na baiwa mutum dama ya kara ma wayarsa sauri
Dukkan wadannan abubuwan , da ma wasu sauran da bamu ambata ba, sune mutum zaya iya samu idan yayi Rooting din wayarsa.
Amma wani hanzari ba gudu ba, mutum ya sanya a ransa cewa, “wayar mutum zata iya samun matsala in har bai bi ka’idar da ta kamata ba wajen yin rooting din”. In har ka san kana da bukatar yi ma wayarka Rooting, to kayi amfani da sahihan manhajojin da ake yin wannan Rooting din da su. Wadannan manhajoji ko kuma applications sun hada da KingRoot, RootMaster da dai sauransu