Mafi yawancin mutane a yanzu sun fi amfani da manhajoji sada zumunci
ko kuma na yin muhawarori win tura sakonni a cikin wayoyinsu, a maimakon
amfani da hanyar da aka sani ta aikawa da karamin sako wanda aka fi
sani da (SMS).
Hakika group chat ya kawo sauki wurin tura sako ga dumbin mutane a
lokaci guda, domin a cikinsa bayan rubutu da muke iya turawa, za kuma mu
iya tura hotuna, bidiyo wani lokaci ma har takardu ana iya turawa, da
wannan dalilin nag a ya dace mu fadawa mutane abubuwa guda goma wadanda
bai kamata muyi amfani da su ba a lokacin da muke mu’amala da mutane a
wurin tattaunawar.
-
Kada ka kirki zauren muhawara mai mutane dayawa.
Mafi yawan manhajoji na tura sako (messaging applications) suna bada
adadin mutanen da zaka iya aikawa sako a cikin zauren muharawa (group
chat). Duk da wasu suna bada damar kari da kauda ido daga adadin da
suka kayyade bai zamo dama garemu ba mu yi ta kirkiran gidaje da dakunan
muhawara barkatai ba. Kasancewar a misali dandalin WhatsApp ya baka
damar saka mutane 190 a matsayin mambobi ba shi ke nuna cewar sai ka
saka kowa da kowa a ciki ba.
Ko da ka kirkiri wannan zaure domin ka rika sanar da wani taro ko
Muhadara ko wa’azi, wani lokaci abin zai baka mamaki idan ka sanar da
wani sako da kake bukatar ayi magana gamsasshiya sai ka samu wadanda ba
su san muhimmancin wannan zaure ba suna iya aikawa da sakon ‘k’ ko kuma
‘okey’.
-
Kada ka saka mutanen da baka sani ba ac ikin group chat din
Ya fi muhimmanci ka saka mutane sanannu wanda kowa a zauren muhawaran
(group chat) ya sansu. Bana son in rika yin magana da kai haka kuma ba
na son ka samu lambar wayata, wannan na daya daga cikin dalilin da ya
sanya bai dace ka dauki duk wanda kake da su a cikin akwatin ajiyar
lambobin wayarka ka saka su a cikin grouph chart ba. Kasancewar lallai
duk wanda ka saka shi a chart to yana da damar ganin lambar kowa da ke
ciki wanda wannan ba zai yi wa wadansu dadi ba.
-
KADA AKYI CHARTING DA MUTUM DAYA KACAL:
Yana da kyau kasan muhimmancin yin magana da kowa da kowa a cikin
zauren muhawara (group chat) ba tare da kebance mutum guda daya ba.
wurin yin maganar da ta shafe ku biyu yafi kyau ace ku kebance a wajan
zauren muhawarar (group chat) din.
Maganar da kowa a zauren yake bukatar ji ita ake yi ac ikin zauren.
-
KADA KA KAWO ZANTUKAN DA BA MUHALLINSU BA:
Yana da kyau ga me charting ya rin ka kawo zantuka gamsassu da suka
dace a inda suka kamata, shi chating ana yin shi ne da abin da ya shafi
aikace aikace hadin kai, taimakon juna da dai makamantansu. Zaka ka iya
fusakntar aikin da aka baka ta yadda zaka kai ga cin masa, zaka iya zama
ka nutsu ta yadda zaka cin ma maufarka.
Shin ko kana tattaunawa game da abin da ya shafi makaranta ta yadda
za ku kara samun jituwa a tsakaninku? Ko kuma hirar dayanku ne a kan
abin da ya shafi zaman ku na karshe, duk abin da bai shafi maudu’in da
aka tsara ba, bai kamata mutum ya shigo da wani magana in ba ta maudu’in
ba.
-
KADA KA TURA KARYA KO ABIN DA BAI KAMATA BA:
Idan kana chating kayi takatsantsan da zantukan daka ke rubutawa tare
da tabbatar da duk abin da ka rubuta ka samo shi daga mattabbata mai
inganci
. Ka da neman sauki ya sa ka rika dauko
ruburu daga wadansu zaurukan ko kuma shafuka kana sakawa a cikin naku
zauren ba tare da ka tantance gaskiyar maganar ba.
-
Kada karubuta banza da
Duk da shafin muhawara ya baka dama ka rubuta abin da ka ga dama,
hakan ba dama bane a gare ka kayita rubuta banza hofi ko maimata abin
da wani ya fada ba. Bai kamata a rubuta abin da bai kamata a cikin wurin
da aka kebance domin tattauna wadansu abubuwa mamu himmanci ba. Misali
za ka ga zaure na addini ne amma sai a sako maganar kwallo, ko kuma
zauren tattaunawa a kan yadda za a bunkasa harkokin lafiya sau kaga wasu
suna saka magana a kan soyayya ko makamantan haka.
-
Kada Kayi shiru
Yin shiru a lokacin da ake tattaunawa a kan abubuwa masu muhimmanci
matsala ce ga mutane da yawa a cikin zaurukan, duk lokacin da aka bijiro
da wani maudu’i mai muhimmancin kuma ake bukatar kowa ya fadi
ra’ayinshi to yana da kyau ka fadi naka ra’ayin, domin kada a zartar da
wani abu da bai kamata ba kuma ka zauna kana korafi daga baya.
-
Kada katura kalma daya a matsayin amsa
Domin neman saukin rubutu kada ka tura rubutu kalma daya saboda za ta
iya daukar ma’ana da yawa ko kuma ayi mata wata fahimta daban da abin
da shi kake nufi ba.
-
Kada ka aika da sako a lokacin da bai kamata ba
Idan ba zaka kira mutum da safe ko da ran aba mai zai sa ka kira shi
can da daddare yana bacci. Idan kasan bai dace a tura sako a lokacin da
ba yini ba ko kafin lokacin bacci yayi, to kayi amfani da wannan dubara
ga manhojojin tura sako.
Mutum zai iya tura sakone kawai alokacin da bai dace ba
idana abune
da yashafi gaggawa wanda ya shafi rayuwan wani. Sannan kuma ka ka sake
ka tura sakon da zai hana ko bata ma wani barcin shi.
-
Fita da ga zaure da zarar an gana abin da aka bude domin shi.
Wannan shi ne abu da mutane da yawa ba su fahimta ba, lallai a na
bude zaurukan ne na wani dan lokaci musamman wadanda ake bude su domin
ganin an gudanar da wani gidauniya domin tallafawa wadansu jama’a ko
kuma irin wanda dalibai za su bude domin ganin sun tattauna tsakaninsu.
To da zarar makasudin da ya sanya aka bude wannan zauren ya kare sai
kowa ya fita daga cikin wannan zaure, ma’ana sai a rufe wannan zauren
domin dalilin bude shi ya riga ya kau. Idan kuma ana ganin cewar ya dace
a ci gaba da yin magana akan wadansu bayanai to yana da kyau a sanar da
mambobi ko kuma a rika haduna ta zahiri ba wai komai a yi shi a boye
ba.
1 Comments
Slot Machines at Borgata 세종특별자치 출장안마 - JTRH Hub. JTRH.com. Your resource to 경기도 출장샵 discover and engage in the 춘천 출장안마 greatest entertainment, gaming, dining, 나주 출장샵 shopping, 통영 출장샵 dining,