Search Bar

BAN-BANCI TSAKANIN NETWORK DA SERVICE


Atsawon lokacin da aka dauka ana amfani da fasahohin DUNIYAR INTERNET DA COMPUTER na zamani, musamman ma wayoyin hannu, akwai wadansu kalmomi guda biyu masu kama da juna ta fuskar amfani da kuma ma’narsu. Wadannan kalmomi sune SERVICE da kuma NETWORK. Tambayar da mutane kan yi akan wadannan kalmomi ita ce, “Wai mi ke bambanci tsakanin SERVICE da kuma NETEWORK”. Mutane da dama sun dade suna neman amsar wannan tambayar daga kwararru a wannan fanni amma basu samu ba. A cikin wannan kasida, zamu fede muku biri har wutsiya dangane da wadannan kalmomi guda biyu da kuma abin da ya bambanta su.
Kafin mu fara bayyana kowanne daga cikin wadannan kalmomi, ya kamata mu fara fahimtar mi ake nufi da Network a mahanga ta ilimin Computer. Idan aka ce Network a fannin ilimin computer, ana nufin duk wata hada ka ko kuma gamayya (waton connection) da akan samar tsakanin computoci ko kuma na’urori biyu ko sama da haka. A nan, computer na nufin ko wane irin abu da za’a iya yin amfani da shi domin sadarwa (wato communication) a tsakanin mutane (kamar na’ura, wayar hannu da dai sauransu). Wannan gamayya (ko kuma connection) da akan yi tsakanin computoci shine ke basu damar su rika musayar bayanai a tsakaninsu (kamar tura sakon murya, video ko kuma rubutu daga wata computer ko wayar hannu zuwa wata). Wannan connection ko kuma gamayya a tsakanin computoci za’a iya yinsa da wire (wired connection) ko kuma ta amfani da tashar iska (wireless connection).
Minene SERVICE?
Dukkan kamfanonin layukan sadarwa da kuka sani, sukan je wuri daban-daban da suke bukatar samar da ayyukansu ga mutanen wajen tare da gina wajen da zasu sanya service ariyarsu (wato communication mast). Wannan service ariya ita ce zata rika kula da dukkan mutanen da a cikin iyakar wurin da ita wannan Ariya take iya kaiwa. A duk idan kaje a wuri, indai har akwai wannan service ariya ta kamfanin layin da kake amfani da shi, to zaka ga wayarka ta ta nuna maka ta hanyar manuniyar service na wayar. Idan kuma ka je inda kamfanin wayarka ba kai ga sanya Ariyarsa ba, to zaka ga service din wayarka ya dauke. Kamar yanda muka fada da farko, babban amfanin service shine domin kula da dukkanin wayoyi ko kuma sauran abubuwan da ake amfani da su wajen sadarwa (kamar computer) da ke keyawan wannan service din. A cikin ko wane service, akwai wasu computoci ko kuma na’urori na musamman da kan baiwa shi wannan service dama ya sadu (communicate) da wasu sauran service din da ke a wannan gari ko kuma yanki.
Minene NETWORK?
Kamar yanda muka fada muku a baya, duk idan har kana a wajen da ke da service na kamfanin layin sadarwar da kake amfani da shi, to tabbas zaka ga service din wayarka ya nuna maka hakan. To amma kuma akwai lokuta da dama da zaku ga duk da cewa akwai service, amma sai mutum ya kasa yin kira, sai ka ji an ce ai babu Network. To a nan, minene wannan network?
Kamar yanda muka fada, a wajen dukkan ko wane service akwai wata na’ura ta musamman (mafi yawanci ana sanya ta a cikin daki) wacce ke bashi dama ya sadu ko kuma yayi connecting da sauran service service da ke a kewayen wannan gari ko kuma yanki. Wannan na’ura ta musamman itace ke bayar da wannan abu da ake kira da Network, wato connection tsakanin dukkanin ariyoyin da kamfanin layi ke da su, da ma sauran wasu ariyoyin mallakar wasu layukan, a cikin gari ko kuma ma kasa baki daya, ta yanda ko daga wace ariya kake zaka iya kiran ko wane mutum da ke a cikin ko wace ariya ta service.
To mi ke bambanci a tsakaninsu?
Muna da tabbancin cewa, ko da barinku muka yi da wannan tambayar, zaku iya amsata. To amma domin yi ma wannan kasida adalci, ya kamata mu amsa wannan tambayar. Shi service shine ke nuna cewa a inda kake akwai service ariya ta layin wayarka, shi kuma network shine ke nuna cewa dukkanin wadannan ariyoyin service na layinka da ma sauran layuka a hada suke, don haka zaka iya kiran dukkan wanda kake bukata ko a ina yake. Amma idan aka samu matsala ya kasance dukkan wadannan ariyoyi ko kuma wasu daga cikinsu ba a hade suke ba (wato babu connection tsakaninsu) shine zaka ji ana cewa babu network (no network) ko kuma akwai ‘yar matsalar network (network problem).
Da fatan wannan sharhi da muka yi ya fitar da ku daga duhu akan ma’ana da kuma bambanci tsakanin wadannan kalmomi guda biyu mabam-banta kuma masu kama da juna, wato SERVICE da kuma NETWORK.

Post a Comment

0 Comments