Tare da mawallafin TASKAR JADDAWA
Amfani da lasifikar kunne ya shahara sosai wajen masu amfani da wayoyin hannu, kwamfuta da rediyo, lasifikar ta na da muhimmanci sosai wajen masu yawan amsa kiran waya, ta inda zasu ɗinga amfani da ita ba tare da sun kara waya a kunnen su ba, amma fa duk lokacin da aka ce sauti mai ƙarfi yana shiga kunnen mutum kai tsaye to akwai matsala sosai, wacce ka iya kawo kurmancewa ma.
Shigar sauti mai Æ™arfi kai tsaye cikin kunnen mutum yana jawo wa dodan kunnen wata girgiza da in ba’a yi sa a ba to an rasa ji Kenan gaba É—aya, akwai matsaloli sosai a amfani da lasifikar kunne wajen yawan amsa kiran waya ko jin waÆ™e-waÆ™e, musamman in ba’a yi amfani da shi yadda ya dace ba.
Wannan rubutan ba anyi shi bane domin hana mutane yin amfani da lasifikar kunne ba, amma tuni da gargaÉ—i ga ma su yawan amfani da lasifikar, saboda lafiya ta fi komi ga ‘dan adam, dole ya zama anyi amfani da lasifikar yadda ya dace domin kaucewa fadawa cikin matsala ta dindindin
In dai akwai kiyaye wajen amfani da lasifikar to lallai za’a ji matuÆ™ar daÉ—in amfani da ita cikin sauki, akwai wasu abubuwa da lasifikar take Æ™unshe da su na cutarwa, kamar guÉ—a huÉ—u wanda za a jero su a Æ™asa.
Tiriri (Radiation): akwai tiririn da lasifikar kunne take fitarwa duk an ce ba shi da wani yawa sosai, amma amfani da lasifikar na tsawon lokaci ya na iya jawo matsaloli sosan gaske, dukkan na’urorin irin waÉ—annan suna fitar da wani tiriri na daban, kuma masana da dama sun gudanar da bincike da ya nuna tiririn na haifar da wasu cuttuka masu hatsarin gaske, misali cutar sankara, cutar Æ™waÆ™walwa, zuÉ“ewar gashin kai, da ma bari ga mata masu juna biyu.
Rasa Ji (hearing loss): wannan yana daga cikin illolin yawan amfani da lasifikar kunne, ta na jawo a rasa ji gaba É—aya, saboda shigar sauti mai Æ™arfi kai tsaye cikin kunnen mutum yana jawo wa dodan kunnen wata girgiza da in ba’a yi sa a ba to an rasa ji kenan gaba É—aya, duk da amfani da lasifikar yadda ya dace ba zai cutar da kunne ba, amma fa daÉ—ewa ana amfani da lasifikar zai jawo kurmancewa ta É—inÉ—inÉ—in wacce ba ta da wani magani, don haka dole a sa lura sosai wajen amfani da lasifikar, a daina Æ™ure sauti ko yaushe, sannan a dinga rage yawan amfani da ita.
Kwayoyin Cuta (Germs): lasifikar kunne wata mafaka ce ta kwayoyin cuta, wani masanin kiwon lafiya kuma farfesa a jam’ar lafiya ta Arizona da ke Amurka, mai suna Kelly Reynolds, ya tabbatar da cewa yawan amfani da lasifikar kunne wajen jin sauti yana Æ™ara barazanar kamowa da kwayoyin cuta, sannan yana jawo wasu kawayoyin cuta masu cutarwa waÉ—anda da mutum ba shi da su, duk da ya ce ba sautin ne yake kawo kwayoyin cutar ba, rashin tsabtace lasifikar yadda ya kamata ne yake jawo taruwar kwayoyin cutar, musamman lasifikar kunne da mutum sama da É—aya suke amfani da ita, in ana tsabtace lasifikar akan kari da
maganin da ya dace to za a kaucewa matsalar kwayoyin cuta ma su haÉ—ari.  

Hana Iska Shiga Cikin Kunne: kamfanoni da suke ƙera lasifikar kunne suna tabbatar da cewa babu wata kafa guɗa daya da suka bari wacce iska za ta iya shiga cikin kunne, domin a cewarsu ta haka ne za a ji sautin yadda ake so, haka na nufin kafin a ji sauti yadda ake so sai an tura lasifikar cikin kunne an tabbatar da an toshe duk wata kafa ta iska, wannan ba ƙaramar barazana ba ce ga dodan kunne, kuma haka zai iya kawo cuttutukan kunne masu dama, sannan ya ƙara yawan ruwan da dodan kunne ya ke fitarwa, tabbas hakan yana kawo wasu matsaloli kamar ciwon kai, ƙaiƙayin kunne, da ciwon kunne mai mugun raɗaɗi, duk da ana iya kaucewa waɗannan matsalolin, misali amfani da lasifikar kunne wacce ta ke da kafar da iska zata iya shiga kunnen, da lasifikar da ake sa ta ta waje waje ba ciki ba, sannan akwai wani soso da wasu daga cikin lasifikokin kunne suke zuwa da shi to wannan soson ya kamata a dinga canza shi lokaci bayan lokaci domin kiyaye lafiyar kunne.