Hausawa kan ce ana zaton wuta a makera sai a same ta a masaka, wannan magana ta yi daidai da yadda a kan yi zaton cewa wasu shafukan internet na kunshe ne da tarin illoli da cututtukan da ka iya lalata ta awasu kuma ba su da shi amma abin ba haka yake ba
Hakika akwai wasu keBantattun shafukan Internet da suka fi ko’ina hatsarin shiga saboda irin abubuwan da ake Boyewa a cikin su, wadanda idan mutum ya ziyarci irin wadannan cututtuka zai iya sanyawa na’urarshi cututtukan da za su iya lalata na’urar da kuma hanyayoyin da za su kiyaye ko su tsare a lokacin da suka fada cikin irin wadannan shafuka.
Mun kasa wadannan shafuka kusan gida biyar (5) wanda za mu sanya alama wacce idan muka sa kafin mu yi bayanin wannan wuri yake nuna cewar illa ko rashin illar shiga wannan shafi. Zai iya yiwuwa bayanai da za mu fadi a wannan Taskar Jaddawa ya zamanto an sami canji sakamakon irin ci gaba da ake yi da kuma gyare-gyaren da wasu shafuka ko kuma gidajen internet suke yi a lokacin da suka fahimci cewar akwai matsaloli tare da shafukan su. Da fatar za a karanta da idon basira kuma a kiyaye, domin manufarmu ita ce a zama babu wata matsala a Kwamfutarmu.
irin hotuna da za ka iya gani na ’yan matan Turawa ko na motoci ko na mawakana iya zama ba hoto ba ne da aka sasu domin kallo kawai, za su iya yuwuwa akwai cutarwa da ke nade a jikinsu. Haka nan mafi yawan amsoshin da mutum kan bincika a shafi na google na iya zama amsa ga mai bincike, zai kuma iya yiwuwa su zama ciwon kai ga computer ka. Jin dadin kallon wasu video da kake yi a internet ko kuma sauko da su (Downloading) jin dadin da annashuwar na iya komawa Bacin rai da damuwa ana’urarka.
Na san sau tari mutum yana jin ana gaya mashi hatsarin da ke cikin shafukan internet, wannan haka yake, wasu shafukan suna da hatsari, wadansu kuma za ka shiga ciki ka yi wadakarka, babu abin da zai same ka. Za ka iya daukar kowane irin mataki domin ka tsare na’urarka, zai yi wahala ya zama kai mai son shiga kowane irin shafi a internet a ce baka kwaso ko da malware ba, ko kuma a kwace ragamar tafiyar da akwatin e mail din ka, a rinka turo maka da sakonni na banza da wofi, ko kuma a kwace maka sirrin da kake ajiyewa ana’urarka, ya zama bayananka, bayanan katin kudin ka, da dai wadansu bayanai wanda baka son kowa ya sani. Irin wadannan dalilai su ne suke sa mutum ya dauki matakin neman tsare kan shi daga fadawa hannun ’yan baranda, wadanda burinsu shi ne su ga sun lalata ko sun kwace ragamar na’urarka ta hanyar virus da malware da dai sauransu. Kuma yana da kyau mutum yasan irin cutar da zai iya samu a lokacin da ya shiga wani shafi, da kuma abin da zai yi domin ya samu tsari kada wani abu a cutar da shi.
Cutar shafukan da ake samu a internet ba iri daya ba ne, godiya ga Allah, Taskar Jaddawa ta yi kokarin bincike kuma ta karkasa su irin wadannan shafuka har gida biyar kamar yadda na fara bayani a farko.
Saboda haka matakin farko shi ne kada ka shiga shafin da baka amince da shi ba, domin yin haka zai iya kawo maka matsala. Ka yi amfani da bayanan da zamu yi maka a matsayin hanyar shiriya.
Flash files da ake zargin suna hade da abin da zai lalata na’urarka.
Inda ake samunsu: Mafi yawancin shafukan da suke amfani da Flash

Ina son mutane kada hankalinsu ya tashi su ce ke nan duk wani shafi da muka gani da flash yana da malware ko virus ke nan. Amsar ita ce a a, domin mafi yawan shafukan da za ka shiga na kasar nan kusa kadan ne wanda ba su da flash a kansu, kuma bana tsammanin akwai wani wanda yake iya yin wannan program da zai cutar a wannan lokaci.
Matakin da za ka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Domin ka tsare kanka daga farmaki irin na flash program, ya kamata ko da wani lokaci ka rinka amfani da gyararran plug-in na flash kuma ya kasance shi plug-in din yana tafiya tare da zamani. (Plug-in shi ne wasu canje-canje da kamfanonin da suke yin software suke yi a kai a kai domin cire wasu matsaloli da mutane suke fuskanta tare da program din su). Sannan za ka iya shirya tsarin yadda kake son idan flash ya sauko daga internet ya zai yi ya yi aiki a cikin na’urarka.
Cuta ta 2:
Gutsattsarin Links wadanda za su iya kai ka ga shafukan da za su iya cutarwa
Inda ake samunsu: Twitter

Abu ne mai sauki mutum ya Boye malware ko kuma cuta a irin wadannan gajerun links. Kuma kusan dukkan irin wadannan gajerun link a karshe suna kai mutum zuwa ga shafin da za ka sami (Trojan horse). Yadda abin yake ka kalli saman browser ka za ka ga inda aka rubuta misali kamar haka (http://www.jaddawa.blogspot.com), a in da ka ga wannan shi ake kira address to zai iya yuwuwa a cikin shafin internet ka ga an rubuta cewar idan ka yi clicking nan misali salisu za ka shiga shafin cin gasa, wato duk inda ka ga rubutu a shafin internet a cikin shafin kuma da layi a kasan shi, shi ake kira link, to yadda su macutan suke yi maimakon idan ka ga wannan link idan ka kai dan yatsan mouse zai iya nuna maka wurin da za ka shiga, to tsarin da Twitter suka yi shi ne maimakon ka ga misali http://www.jaddawa.blogspot.com sai kawai ka ga http:// kawai.
Matakin da za ka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Abu mafi sauki shi ne idan ka ga wannan link din kada ga latsa shi. Na san kuwa abin zai baka dariya domin an hanaka yawo a twitter kenan? Wata hanyar da za ka bi kuma itace ka yi amfani da kananan application da ake attaching din su da Twitter wanda su suna taimaka wa wajen biyyana asali sannan cikakkiyar hanyar da wannan link zai kai ka. Amma shawara mafi inganci idan har ba ka san waye ya aiko maka da link ba, kuma baka san inda wannan link zai kai ka ba, abu mafi dacewa shi ne ka rabu da shi.
Cuta ta 3:
Sakon email da ga macuta ko kuma attachment da zai kai ga inda za’a kwashe maka muhimman bayanai ko kuma ka dibo Virus
Inda ake samunsu: Akwatin Email din ka

Matakin da za ka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Kada ka yarda da ko wani irin sakon da baka san waye ya aiko maka ba, ko kuma ba ka yi magana da su za su aiko maka ba. Idan har ka ga irin wannan sako kuma kana bukatar ka fahimci ina aka sa gaba, to, sai ka ki latsa wannan Link, ka shiga website da ka ji cewar suke da alhakin wannan sako idan sakon saboda kai ne, to, ka ga babu matsala.
Cuta ta 4:
Malware da ake boye su a jikin Video ko Music ko kuma Software wajen Downloading
Inda ake samunsu: Shafukan Torrent

Ben Edelman wanda yake sashin bincike sannan kuma Farfesa ne a Harvard Business School ya ce “Ina ganin babu wani shafi a Internet wanda ya fi ko ina hatsarin shiga irin gidajen Torrent, domin su ba su da doka a kan abin da ake zuba masu, domin ba a sayar da kaya a ciki. Shi yasa nake ganin shafukan da suke nuna tsiraici za su fi shafukan Torrent tsabta, idan ka dangantasu da cewar ana biyan su kudi domin amfani da kayansu”. In ji Ben Edel-man.
Matakin da za ka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Hanya mafi dacewa ita ce, kada ka shiga wannan shafi, sannan kuma ka guji irin wadannan kayayyakin da ba su da garanti wajen amincin wadanda suka bayar da su. Amma idan har ka dage a kan cewar dole sai ka shiga, to, ka yi amfani da wata na’urar da ka san babu muhimman bayanan ka a cikin ta. Kuma ya kasance idan za ka saukar da kaya daga irin wadannan shafuka ka rinka kokarin karanta jawaban da mutane suke yi a kasan shafin, idan kayan da kake son ka yi downloading akwai matsala za ka ji idan akwai wani matsala, idan kuma babu matsala za ka ji shi ma. Idan kuma dai ka nace sai ka dauko shi, kuma babu wanda ya yi bayanin lafiyarshi? To, idan ka saukar sai ka jira sai bayan kamar kwana biyu, sai ka bude shi. Amma shi ma da sharadi ya zamanto kana amfani da Anti-Virus mai lasisi kuma ya zama ko da wanne lokaci kana Updating na anti-virus din.
Cuta ta 5:
Malware a cikin Hotuna ko Video wanda akwai tsiraici a cikin shi.
Inda ake samunsu: Amintattun Gidajen nuna tsiraici

Kamar yadda na fadi a baya, amintattun shafukan nuna tsiraici, yana da matukar wahala su bari a saka Malware a ciki, domin suna son ko da wani lokaci abokanen huldansu su ci gaba da hulda da su. Amma yana da wahala ka iya raba tsakanin amintattun shafukan batsa da malware.
Matakin da za ka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Kayi hankali da irin Video da za ka sauko da shi, kuma ka kiyaye dukkan wani Video da zai ce sai ya dauko Codecs sannan ka iya amfani da shi, ko kuma ka yi amfani da toolbar irin na Norton ko McAfee da SiteAdvisor da ke Firefox domin idan akwai gidan da za ka shiga akwai matsala su fada maka.
Wani mataki na biyu shi ne idan har ka ce za ka shiga wannan shafi, to ka yi amfani da wani computer domin tsaron mutuncin ka da na iyalanka.
Cuta ta 6
Trojan Horses wanda ake wufintar da mutum a matsayin video codecs, daga karshe malware su shiga computer dinka.
Inda ake samunsu: Websites da ake saukar da Video, ko kuma a peer-to-peer networks.

Matakin da za ka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Mataki mai kyau shi ne ka tabbatar dukkan wani abu da za ka kalla kai tsaye a internet idan ya ce kana bukatar codecs wajen kallon shi kasan su wane ne masu video din, kamar misalin video’n da ake samu a dandalin YouTube.com da kuma Vimeo idan ka ga sun ce kana bukatar codecs za ka iya saukar da su domin su amintattun gidajen ne, haka nan kamar gidajen ka amince da su cewar ba za su saka tsiya a cikin website dinsu ba, ko kuma site da ka san ka biya kudi ne ka ke kallon abin da suka saka. Amma kuma idan kai ma’abocin kallo ne, ko da wane lokaci kana son kallon wasanni ko kuma labarin ko kuma irin shirye-shiryen wasan kwaikwayo irin daga gidajen Hulu.com ko TV.com ko kuma ABC.com da kuma iTunes.com to su ma suna da aminci domin sunfi peer-to-peer network .
Cuta ta 7
Taswira a jikin wayarka wacce take baka damar ganin wurare daga jikin ta.
Inda ake samunsu: A wannan wayarka mai tsada (Smartphones)

Dangane da irin wannan misalan, tabbas akwai application da suke da amfani a cikin smartphone kamar wanda zai iya gaya maka wajen da ka nufa, ko kuma ka sauka a wani gari da baka sanshi ba zai iya fada maka wajen da kake da kamar misalin hotel ko kuma dakin abinci da ke kusa da kai. Kodayake kamfanin Apple masu yin irin su IPhones kwanakin baya suka kara kaimi wajen ganin sun kiyaye mutuncin masu amfani da kayansu, tun daga abin da ya shafi bayanan sirrin su, sunayensu da wurin da yake da dai makamantansu.
Matakin da za ka dauka idan ka ziyarci wannan shafi
Mataki mai kyau shi ne ka kiyaye da dukkan wani sabon abu da baka sanshi ba, ko kuma ka lura da kyau da irin hotunan da suke bayyana a fuskar smartphone dinka, sannan kuma ya kasance ba kowane irin application za ka gani ba kamar daga facebook.com ko kumaFourSquare wanda suke nuna maka wurare a yarda da shi ba, sannan kuma ya kasance kana da cikakkiyar masaniyar inda za ka shiga.
0 Comments