Kotun kolin Pakistan ta sake haramta kallon dukkan tasoshin talbijin din India a kasar, inda ta yi fatali da hukuncin da wata karamar kotu ta yanke tun da fari.
Mai shari'a Saqib Nisar ya ce hukuncin da suka yanke ya dace saboda India tana hana ruwa kwarara daga cikin ta zuwa Pakistan.
Pakistan ta ce an hana madatsun ruwan kwarara cikin kasar ne a matsayin wani makami na musgunawa, ko da yake India ta musanta zargin.
Gidajen talbijin da fina-finan India sun yi fice a kasar Pakistan, ko da yake a baya ma an hana kallon su a kasar lokacin da aka samu wata rashin jituwa.
Rahotanni sun ambato Mr Nisar na cewa "Ruwan da Pakistan ke samu daga India na ci gaba da yankewa," a lokacin da yake kawar da hukuncin da babbar kotun da ke Lahore ta yanke. "Don me ba za mu rufe tasoshin talbijin dinsu ba?"
India na samun fiye da kashi 80 cikin 100 na ruwan da take amfani wurin noman rani daga kogin Indus na kasar Pakistan, wanda akasari yake kwaranyawa daga tuddai.
A shekarar 1965 ne Pakistan ta soma haramta kallon fina-finan India a kasarta sakamakon yakin da kasashen biyu suka yi.
Amma an dage annan haramci a 2008, ko da yake akan sake sa wa sannan a cire a kai-a kai.
A 2016 Pakistan ta haramta kallon tasoshin talbijin na India lokacin da jami'an tsaron India suka yi dirar mikiya kan masu zanga-zanga a yankin Kashmir da ake takaddama a kansa.