Search Bar

An ga sauran ’yan matan Chibok da aka sace a yau 28/10/2018


Iyayen 'yan matan Chibok da aka sace a 2014 sun ce an ga 57 daga cikin wadanda suka rage a hannun Boko Haram a Jamhuriyar Kamaru.
Shugaban kungiyar iyayen 'yan matan Yakubu Nkeki ne ya tabbatar wa BBC wannan labarin.
A cewar sa wata mata da ta tsere daga hannun mayakan Boko Haram a watan Yuni a Kamaru ta shaida musu cewa ana tsare da matan ne a kauyukan Garin Magaji da Garin Mallam da ke yankin Marwa na arewacin kasar
Matar ta ce an aurar da dukkan matan ga mayakan Bokon Haram kuma da dama daga cikinsu sun haihu, in ji Nkeki.
Shugaban kungiyar iyayen 'yan matan Chibok din ya ce sun gaskata kalaman matar saboda ta gaya musu sunayen matan
Ya ce matar ta shaida musu cewa yanayin da matan ke ciki ba mai kyau ba ne, domin ba sa samun isasshen abinci.
Har yanzu 'yan matan na Chibok 112 cikin 276 da aka sace ne basu koma gida ba.
An sace matan ne lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, lamarin da ya jawo Allah wadai daga kusan dukkan sassan duniya.




Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi alkawarin ceto dukkansu sai dai har yanzu ba ta cika wannan alkawarin ba ko da ya ke ta yi nasarar ceto fiye da 100 daga cikin 'yan matan.

Post a Comment

0 Comments