Gwamnan jihar Kaduna da ke Najeriya Nasir Elrufai ya ce zai tashi Gonin Gora dungurungun idan matasan garin suka ci gaba da tare mutane suna kashe su.
Garin na Gonin Gora yana kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, kuma matasan garin sun sha tare matafiya suna kashe su da zaar an soma rikici a birnin Kaduna.
Da yake jawabi a filin "Hannu a Yawa" na gidan rediyon tarayya na Kaduna, Gwamna Elrufai ya ce "ina ba mutanen Gonin Gora shawara cewa wannan abin da matasansu suke yi su daina idan ba haka ba wallahi tallahi zan tashi garin
"Ba za mu yarda su rika rufe hanya su hana mutane shiga ko fita daga gari suna kashe su ba. Za mu sa jami'an tsaro su rika duba wurin amma idan ba su daina ba, garin da kan shi bai fi karfin gwamnati ba."
Gwamnan na Kaduna ya yi wannan jawabi ne daidai lokacin da gwamnatin jihar ta ce 'yan sanda sun cafke mutum 32 wadanda ake zargi da hannu a rikicin jihar.
Wata sanarwa da Samuel Aruwan, mai magana da yawun gwamnan jihar Malam Nasir Elrufai ya aike wa manema labarai ta ce jami'an tsaron sun dakile wani yunkuri na tayar da hankali a wuraren ibada da ke unguwannin Kawo da Hayin Banki da ke cikin birnin Kaduna.
Kazalika an sake kashe mutum daya a Kasuwan Magani kana aka kama wani mutum da tsakar dare dauke da bindiga, in ji sanarwar.
Mr Aruwan ya ce "za a gudanar da bincike kan mutanen sannan a gufrfanar da su gaban kuliya."
1 Comments