Fasahar wayoyin hannu ta wannan zamani na samun cigaba, wanda wayar ta zamanto ‘karamar na’ura mai kwakwalwa, ana kiransu smart phone a turance, suna da muhimmanci kwarai da gaske inda ke amfani dasu wajen sanum bayanai a yanar gizo, sauraren wakoki, karata sakonnin email da dai sauransu.
Masu bincike sun ce dandazon manhajar dake cikin wayoyin hannu na wannan zamani a kwai injimin gano girgizar kasa a yawancin wayoyin, wanda wayar ka iya kaiwa ga ceton rayuwar mutane ta hanyar gargadin su alokacin da girgirzar kasa ke kokarin faruwa.
Yawancin kasashen dake samun yawan girgizar kasa a duniya da suka hada da Japan da Amurka da sauran kasashe suna da manyan cibiyoyin sadarwa, wanda wayoyin su ke hade da wani karamin firikwensi cikin waya da zata iya gano halin da ‘kasa ke ciki, alokacin girgizar kasa.
Yawancin mutanen duniyar na rike da wayoyin hannu na zamani, wadanda ke cike da manhajoji dabam dabam, dake taimakawa mutane a wannan zamani.
0 Comments